26 Magabciyar ƙarshe da za a shafe, ita ce mutuwa.
27 “Gama Allah ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa.” Amma da aka ce, “An sarayar da kome karƙashin ikonsa” a fili yake shi wannan da ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa ɗin, a keɓe yake.
28 Sa'ad da kuma aka sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa ɗin, sa'an nan ne Ɗan da kansa shi ma zai sarayar da kansa ga wannan da ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa, domin Allah yă tabbata shi ne kome da kome.
29 In ba haka ba, mene ne nufin waɗanda ake yi wa baftisma saboda matattu? In ba a ta da matattu sam, don me ake yi wa waɗansu baftisma saboda su?
30 Don me kuma nake a cikin hatsari a kowane lokaci?
31 Na hakikance 'yan'uwa, saboda taƙama da ku da nake yi a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu, a kowace rana sai na sallama raina ga mutuwa!
32 Idan bisa ga ra'ayin mutum ne, na yi kokawa da namomin jeji a Afisa, mece ce ribata in dai har ba a ta da matattu? “Ba sai mu yi ta ci da sha ba, da yake gobe za mu mutu?”