15 To, 'yan'uwa, kun sani fa jama'ar gidan Istifanas su ne nunan fari a ƙasar Akaya, sun kuwa ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima.
16 Ina roƙonku ku yi wa irin waɗannan mutane biyayya, har ma ga duk waɗanda suke abokan aikinmu da wahalarmu.
17 Na yi farin ciki da zuwan Istifanas, da Fartunatas, da Akaikas, domin sun ɗebe mini kewarku.
18 Sun dai wartsakar da ni da kuma ku. Sai ku kula da irin waɗannan mutane.
19 Ikilisiyoyin ƙasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikkilisiyar da take taruwa a gidansu, suna gaishe ku da kyau da kyau saboda Ubangiji.
20 Dukan 'yan'uwa suna gaishe ku. Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba.
21 Ni Bulus, ni nake rubuta gaisuwar nan da hannuna.