3 Ina kuma tare da ku ne da rauni, da tsoro, da rawar jiki ƙwarai.
4 Jawabina da wa'azina, ba su danganta ga maganar rarrashi ko ta wayo ba, sai dai ga rinjaye na ikon Ruhu,
5 kada bangaskiyarku ta dogara ga hikimar mutane, sai ga ƙarfin Allah.
6 Duk da haka dai muna sanar da hikima ga waɗanda suka kammala, sai dai ba hikimar wannan zamani ba, ba kuwa ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda suke shuɗewa ba.
7 Amma muna maganar asirtacciyar hikima ta Allah, wadda dā ɓoyayyiya ce, wato, hikimar da Allah ya ƙaddara tun gaban farkon zamanai, domin ɗaukakarmu.
8 A cikin masu mulkin zamanin nan, ba wanda ya gane hikimar nan, don da sun gane ta, da ba su gicciye Ubangiji Maɗaukaki ba.
9 Amma kuwa yadda yake a rubuce ke nan cewa,“Abubuwan da ido bai taɓa gani ba,Kunne bai taɓa ji ba,Zuciyar mutum kuma ba ta ko riya ba,Waɗanda Allah ya tanadar wa masu ƙaunarsa,”