4 In kuwa kuna da irin waɗannan ƙararraki, don me kuma kuke kai su gaban waɗanda su ba kome ba ne, a game da Ikkilisiya?
5 Na faɗi wannan ne don ku kunyata. Ashe, wato, ba ko mutum ɗaya mai hikima a cikinku, da zai iya sasanta tsakanin 'yan'uwa?
6 Amma ɗan'uwa yakan kai ƙarar ɗan'uwa, gaban marasa ba da gaskiya kuma?
7 Ku yi ƙarar juna ma, ai, hasara ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura a zambace ku?
8 Amma, ga shi, ku da kanku kuna cuta, kuna zamba, har ma 'yan'uwanku kuke yi wa!
9 Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo,
10 ko ɓarayi, ko makwaɗaita, ko mashaya, ko masu zage-zage, ko mazambata, da za su sami gādo a cikin Mulkin Allah.