29 Abin da nake nufi 'yan'uwa, lokacin da aka ƙayyade ya ƙure. A nan gaba masu mata su zauna kamar ba su da su,
30 masu kuka kamar ba kuka suke yi ba, masu farin ciki ma kamar ba farin ciki suke yi ba, masu saye kuma kamar ba su riƙe da kome,
31 masu moron duniya kuma, kada su ba da ƙarfi ga moronta. Don yayin duniyar nan mai shuɗewa ne.
32 Ina so ku 'yantu daga damuwa. Mutum marar aure yakan tsananta kula da sha'anin Ubangiji, yadda zai faranta wa Ubangiji rai.
33 Mutum mai aure kuwa, yakan tsananta kula da sha'anin duniya, yadda zai faranta wa matarsa rai.
34 Hankalinsa ya rabu biyu ke nan. Mace marar aure, ko budurwa, takan tsananta kula da sha'anin Ubangiji, yadda za ta kasance tsattsarka a jiki, da kuma a rai. Mace mai aure kuwa takan tsananta kula da sha'anin duniya, yadda za ta faranta wa mijinta rai.
35 Na faɗi haka ne, don in taimake ku, ba don in ƙuntata muku ba, sai dai don in kyautata zamanku, da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.