1 Ni ba ɗa ba ne? Ba kuma manzo ba ne? Ban ga Yesu Ubangijinmu ba ne? Ku ba aikina ba ne a cikin Ubangiji?
2 Ai, ko waɗansu ba su ɗauke ni a kan manzo ba, lalle ku kam, ni manzo ne a gare ku, domin kuwa ku ne tabbatar manzancina a gaban Ubangiji.
3 Wannan ita ce kariyata ga masu son tuhumata.
4 Ashe, ba mu da iko a ba mu ci da sha?
5 Ba mu da ikon tafiya da matarmu ta aure mai bi, kamar yadda sauran manzanni, da 'yan'uwan Ubangiji, da kuma Kefas suke yi?
6 Ko kuwa dai ni da Barnaba ne kawai, ba mu da iko a ɗauke mana aikin ci da kai?
7 Wa yake yin aikin soja, sa'an nan yă ci da kansa? Wa zai shuka garkar inabi, yă kasa cin 'ya'yan? Wa zai yi kiwon garke, yă kasa shan nonon?