3 Gama wannan shi ne nufin Allah, wato ku yi zaman tsarki, ku guje wa fasikanci,
4 kowannenku kuma ya san yadda zai auro matarsa da tsarki da mutunci,
5 ba ta muguwar sha'awa ba, yadda al'ummai suke yi, waɗanda ba su san Allah ba.
6 A cikin wannan al'amari kuwa kada kowa ya keta haddi, har ya cuci ɗan'uwansa, domin Ubangiji mai sakamako ne a kan dukkan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka gargaɗe ku, muka tabbatar muku tun da wuri.
7 Ai, ba a zaman ƙazanta ne Allah ya kira mu ba, amma ga zaman tsarki ne.
8 Saboda haka, kowa ya ƙi yarda da wannan, ba mutum ya ƙi ba, amma Allah ya ƙi, shi da yake ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.
9 A game da ƙaunar 'yan'uwa kuma, ba lalle sai wani ya rubuto muku ba. Ai, ku kanku ma, Allah ya koya muku ku ƙaunaci juna.