1 Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu bisa ga umarnin Allah Mai Cetonmu, da kuma na Almasihu Yesu abin begenmu,
2 zuwa ga Timoti, ɗana na hakika, ta wajen bangaskiya.Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.
3 Kamar yadda na roƙe ka, ka dakata a Afisa sa'ad da za ni ƙasar Makidoniya, ka gargaɗi waɗansu mutane kada su koyar da wata koyarwa dabam,
4 kada kuma su ɓata zarafinsu a wajen almara da yawan ƙididdigar asali marar iyaka, waɗanda sukan haddasa gardandami, a maimakon riƙon amanar al'amuran Allah da bangaskiya.
5 Alhali kuwa manufar gargaɗinmu ƙauna ce, wadda take bulbulowa daga tsarkakakkiyar zuciya, da lamiri mai kyau, da kuma sahihiyar bangaskiya.
6 Waɗansu sun kauce wa waɗannan al'amura, har sun bauɗe, sun shiga zancen banza.
7 Suna burin zama masanan Attaura, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle matsalar da suke taƙamar haƙiƙicewa a kai.