3 Wannan kyakkyawan abu ne, kuma abin karɓa ne a gun Allah Mai Cetonmu,
4 wanda yake son dukkan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.
5 Domin Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya ne, a tsakanin Allah da mutane, Almasihu Yesu, mutum,
6 wanda ya ba da kansa fansa saboda kowa da kowa. An kuwa yi shaidar wannan a daidai lokacinsa.
7 Don haka ne aka sa ni mai wa'azi, da manzo kuma (gasikya nake faɗa, ba ƙarya ba), mai koya wa al'ummai al'amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.
8 Saboda haka, a kowane wuri ina so maza su yi addu'a, suna ɗaga hannuwa tsarkakakku, ba tare da fushi ko jayayya ba.
9 Mata kuma su riƙa sa tufafin da suka dace da su saboda kunya da kamunkai, ba adon kitso, ko kayan zinariya, ko lu'ulu'u, ko tufafi masu tsada ba,