1 Duk ɗaukacin masu igiyar bauta a wuyansu, su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci a girmama su matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwar nan.
2 Waɗanda suke da iyayengiji masu ba da gaskiya, kada su raina su, domin su 'yan'uwa ne a gare su. Sai ma su ƙara bauta musu, tun da yake waɗanda suke moron aikin nan nasu masu ba da gaskiya ne, ƙaunatattu kuma a gare su.Ka koyar da waɗannan abubuwa, ka kuma yi gargaɗinsu.
3 Duk wanda yake wata koyarwa dabam, bai kuwa yarda da sahihiyar maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma koyarwar da ta dace da bautar Allah ba,
4 girmankai ya ciccika shi ke nan, bai san kome ba, yana da muguwar jarabar gardama da jayayya a kan maganganu kawai, waɗanda suke jawo hassada, da husuma, da yanke, da mugayen zace-zace,
5 da kuma yawan tankiya a cikin mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda har gaskiya ta ƙaurace musu, suna tsammani bin Allah hanya ce ta samu.
6 Bin Allah a game da wadar zuci kuwa riba ce mai yawa.