23 Ba mai ƙin Ɗan ya sami Uban. Kowa ya bayyana yarda ga Ɗan, ya sami Uban ke nan.
24 Ku kam, abin da kuka ji tun da farko, sai ya zauna a zuciyarku. In abin da kuka ji tun farko ya zauna a zuciyarku, ku ma sai ku zauna cikin Ɗan, da kuma Uban.
25 Wannan shi ne alkawarin da ya yi mana, wato, rai madawwami.
26 Ina rubuto muku wannan ne a kan waɗanda suke ƙoƙarin ɓad da ku.
27 Ku kam, shafar nan da kuka samu daga Ruhu Mai Tsarki tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafar nan tasa take koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.
28 To a yanzu, ya ku 'ya'yana ƙanana, sai ku zauna cikinsa, domin sa'ad da ya bayyana, mu kasance da amincewa, kada kunya ta rufe mu a gabansa a ranar komowarsa.
29 Da yake kun san shi mai adalci ne, ku dai tabbata duk mai aikata adalci haifaffensa ne.