1 Ya ku ƙaunatattuna, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku jarraba ku gani ko na Allah ne, don annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya.
2 Ta haka za ku san Ruhun Allah, wato, duk ruhun da ya bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana ne da jiki, shi ne na Allah.
3 Duk ruhun kuwa da bai bayyana yarda ga Yesu ba, ba na Allah ba ne, wannan shi ne ruhun magabcin nan na Almasihu wanda kuka ji zai zo, a yanzu ma har yana duniya.
4 Ya ku 'ya'yana ƙanana, ku kam na Allah ne, kun kuma ci nasara a kan waɗannan, domin shi wanda yake zuciyarku ya fi wanda yake duniya ƙarfi.
5 Su kuwa na duniya ne, shi ya sa suke zance irin na duniya, duniya kuwa tana sauraronsu.