11 Ta haka kuma, za a ba ku cikakken 'yancin shiga madawwamin mulki na Ubangijinmu Mai Cetonmu Yesu Almasihu.
12 Don haka, lalle kullum ba zan fasa yi muku tunin waɗannan abubuwa ba, ko da yake kun san su, kun kuma kahu a kan gaskiyar nan da kuke da ita.
13 A ganina daidai ne, muddin ina raye a cikin jikin nan, in riƙa faɗakar da ku ta hanyar tuni,
14 da yake na sani na yi kusan rabuwa da jikin nan nawa, kamar yadda Ubangijinmu Yesu Almasihu ya yi mini ishara.
15 Aniyata ce, a kowane lokaci ku iya tunawa da waɗannan abubuwa bayan ƙauracewata.
16 Ai, ba tatsuniyoyi da aka ƙaga da wayo muka bi ba, sa'ad da muka sanar da ku ikon Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma bayyanarsa, ɗaukakarsa ce muka gani muraran.
17 Domin sa'ad da Allah Uba ya girmama shi, ya kuma ɗaukaka shi, sai murya ta zo masa daga mafificiyar ɗaukaka cewa, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai,”