9 Domin duk wanda ya rasa halayen nan, to, makaho ne ko kuwa ganinsa dishi-dishi ne, ya kuma mance an tsarkake shi daga zunubansa na dā.
10 Saboda haka, ya ku 'yan'uwa, ku ƙara ba da himma ku tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Domin in kun bi waɗannan halaye, ba za ku fādi ba har abada.
11 Ta haka kuma, za a ba ku cikakken 'yancin shiga madawwamin mulki na Ubangijinmu Mai Cetonmu Yesu Almasihu.
12 Don haka, lalle kullum ba zan fasa yi muku tunin waɗannan abubuwa ba, ko da yake kun san su, kun kuma kahu a kan gaskiyar nan da kuke da ita.
13 A ganina daidai ne, muddin ina raye a cikin jikin nan, in riƙa faɗakar da ku ta hanyar tuni,
14 da yake na sani na yi kusan rabuwa da jikin nan nawa, kamar yadda Ubangijinmu Yesu Almasihu ya yi mini ishara.
15 Aniyata ce, a kowane lokaci ku iya tunawa da waɗannan abubuwa bayan ƙauracewata.