15 Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu.
16 Wato niyyata in bi a kanku in za ni Makidoniya, in kuma komo wurinku daga Makidoniya, sa'an nan ku yi mini rakiya in zan tafi Yahudiya.
17 Ashe, a lokacin da na yi niyyar yin haka, wato na nuna rashin tsai da zuciya ke nan? Ko kuwa shiririta nake yi kawai irin ta halin mutuntaka, in ce, “I” in koma in ce, “A'a”?
18 Yadda ba shakka Allah yake mai alkawari, haka ma maganar da muka yi muku, ba shiririta a ciki.
19 Domin kuwa, Ɗan Allah, Yesu Almasihu, wanda ni, da Sila, da Timoti muka yi muku wa'azi, ai, ba shiririta a game da shi, har kullum a kan gaskiya yake.
20 Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi take, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah.
21 Domin kuwa, Allah shi ne mai tabbatar da mu da ku gaba ɗaya ga Almasihu, shi ne wanda ya shafe mu kuma.