1 Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali'u da sanyin hali na Almasihu, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” ne a cikinku, amma “mai matsawa” ne sa'ad da nake rabe da ku,
2 ina roƙonku kada ku tilasta ni in matsa muku sa'ad da na zo, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha'anin duniya ne.
3 Ko da yake a cikin jiki muke tafiya, famarmu ba irin na mutuntaka ba ne.
4 Don kuwa makamanmu na fama ba na mutuntaka ba ne, na ikon Allah ne, masu rushe maƙamai masu ƙarfi.
5 Muna ka da masu hujjoji a cikin zace-zacensu, muna rushe kowace ganuwar alfarma mai tare sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Almasihu.