1 Wannan shi ne zai zama zuwana na uku a gare ku. Lalle ne kuwa a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.
2 Na gargaɗi waɗanda suka yi zunubi a dā, da kuma saura duka, a yanzu kuma da ba na nan ina yi musu gargaɗi, kamar yadda na yi sa'ad da nake nan a zuwana na biyu, cewa in na sāke zuwa ba zan sawwaƙe musu ba.
3 In dai nema kuke yi ku tabbata, cewa da izinin Almasihu nake magana, to, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku.
4 Ko da yake an gicciye shi ne da rashin ƙarfi, duk da haka a raye yake ta ikon Allah. Mu ma marasa ƙarfi ne kamarsa, amma a game da al'amuranku da za mu zartar, a raye muke tare da shi, ta ikon Allah.
5 Ku jarraba kanku ku gani, ko har yanzu kuna a raye da bangaskiya. Ku riƙa auna kanku. Ashe, ba ku tabbata Almasihu yana a cikinku ba? Sai ko in kun kasa ga gwajin!
6 Muna fata ku gane, mu ba mu kāsa ba.