8 Ina misalin fifikon hidimar Ruhu mafi ɗaukaka?
9 Gama idan hidimar da take jawo hukunci abar ɗaukakawa ce, to, lalle hidimar da take jawo samun adalcin Allah ta fi ta ɗaukaka nesa.
10 Hakika a wannan hali, abin da dā take da ɗaukaka ya rasa ɗaukaka sam, saboda mafificiyar ɗaukakar da ta jice ta.
11 Domin in aba mai shuɗewa an bayyana ta da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwamamme, lalle ne ya kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa.
12 Tun da yake muna da sa zuciya irin wannan, to, muna magana ne gabanmu gaɗi ƙwarai.
13 Ba kamar Musa muke ba, wanda ya rufe fuskarsa da mayafi, don kada Isr'ailawa su ga ƙarewar ɗaukakar nan mai shuɗewa.
14 Amma hankalinsu ya dushe, domin har ya zuwa yau, in ana karatun Tsohon Alkawari, mayafin nan har yanzu ba a yaye yake ba, domin ba ya yayuwa sai ta wurin Almasihu kaɗai.