3 gama in aka suturta mu da shi, ba za a same mu tsirara ba.
4 Sa'ad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, amma don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa.
5 Allah kuwa shi ya tanadar mana wannan sākewar, shi da ya ba mu Ruhunsa, domin tabbatar da abin da zai yi a nan gaba.
6 Saboda haka, kullum muke da ƙarfin zuciya, mun kuma sani, muddin muna tare da wannan jiki, a rabe muke da Ubangiji,
7 domin zaman bangaskiya muke yi, ba na ganin ido ba.
8 Hakika muna da ƙarfin zuciya, mun kuma gwammace mu rabu da jikin nan, mu zauna a gun Ubangiji.
9 Saboda haka, ko muna gunsa, ko muna a rabe da shi, burinmu shi ne mu faranta masa zuciya.