1 To, 'yan'uwa, muna so mu sanar da ku alherin Allah da ya bayar a cikin ikilisiyoyin Makidoniya,
2 wato, ko da yake an gwada su da matsananciyar wahala, suna kuma a cikin baƙin talauci, duk da haka, yawan farin cikinsu, har ya kai su ga yin alheri ƙwarai da gaske.
3 Domin na tabbata daidai ƙarfinsu suka bayar, har ma fiye da ƙarfinsu ne, da ra'insu kuma.
4 Sun roƙe mu ƙwarai da gaske mu yi musu alheri su ma, a sa su a cikin masu yi wa tsarkaka gudunmawa,
5 har ma suka bayar fiye da yadda muka zata, amma sai da suka fara miƙa kansu ga Ubangiji da a gare mu kuma, bisa ga nufin Allah.