1 Na gama ka da Allah, da kuma Almasihu Yesu, wanɗa zai yi wa rayayyu da matattu shari'a, na kuma gargaɗe ka saboda bayyanarsa da kuma mulkinsa,
2 ka yi wa'azin Maganar Allah, ka dimanta a kai ko da yaushe, kana shawo kan mutane, kana tsawatarwa, kana ƙarfafa zukata, a game da matuƙar haƙuri da kuma koyarwa.
3 Don lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu yana ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu.
4 Za su toshe kunnensu ga jin tatsuniyoyi.
5 Kai kuwa, sai ka natsu a cikin kowane hali, ka jure wa shan wuya, kana aikin mai bishara, ka cika hidimarka.
6 Ni fa tsiyaye ni ake yi kamar hadaya, lokacin ƙauracewata kuma ya gabato.
7 Na sha fama, famar gaske, na gama tseren, na riƙe bangaskiya.