1 Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya, da 'ya'yanta waɗanda nake ƙauna da gaske, ba kuwa ni kaɗai ba, har ma dukan waɗanda suka san gaskiya,
2 wato, muna ƙaunarku saboda gaskiyar da take a dawwame a cikinmu, za ta kuwa kasance tare da mu har abada.
3 Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uban, da kuma na Yesu Almasihu Ɗan Uban, za su tabbata a gare mu, da gaskiya da ƙauna.
4 Na yi farin ciki ƙwarai da samun waɗansu 'ya'yanki suna bin gaskiya, kamar yadda Uba ya ba mu umarni.
5 Yanzu kuma ina roƙonki, uwargida, ba cewa wani sabon umarni nake rubuto miki ba, sai dai wanda muke da shi tun farko ne, cewa mu ƙaunaci juna.