1 An yi wani mutum a Kaisariya, mai suna Karniliyas, wani jarumi ne na ƙungiyar soja da ake kira Ƙungiyar Italiya.
2 Shi kuwa mutum ne mai ibada, yana tsoron Allah shi da iyalinsa duka, yana yana ba jama'a sadaka hanu sake, yana kuma addu'a ga Allah a kai a kai.
3 Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma, ya ga wani mala'ikan Allah a fili cikin wahayi, ya shigo, ya ce masa, “Ya Karniliyas.”
4 Shi kuwa ya zura masa ido a tsorace, ya ce, “Ya Ubangiji, mene ne?” Mala'ikan kuma ya ce masa, “Addu'arka da sadakarka sun kai har a gaban Allah, abubuwan tunawa ne kuma a gare shi.
5 To, yanzu, sai ka aiki mutane Yafa su kirawo Saminu, wanda ake kira Bitrus,
6 ya sauka a gun Saminu majemi, wanda gidansa yake a bakin bahar.”