24 Kashegari kuma suka shiga Kaisariya. Dā ma Karniliyas na tsammaninsu, har ya gayyato 'yan'uwansa da aminansa.
25 Bitrus na shiga gidan ke nan sai Karniliyas ya tarye shi, ya fāɗi a gabansa, ya yi masa sujada.
26 Amma Bitrus ya tashe shi, ya ce, “Tashi, ai, ni ma ɗan adam ne.”
27 Bitrus na zance da shi, ya shiga ya tarar mutane da yawa sun taru.
28 Ya ce musu, “Ku da kanku kun sani, bai halatta Bayahude ya cuɗanya, ko ya ziyarci wani na wata kabila dabam ba. Amma Allah ya nuna mini kada in ce da kowa marar tsarki, ko mai ƙazanta.
29 Saboda haka da aka neme ni, na zo, ban ce a'a ba. To, yanzu ina so in ji abin da ya sa kuka kira ni.”
30 Sai Karniliyas ya ce, “Yau kwana uku ke nan, wajen war haka, ina addu'ar ƙarfe uku na yamma a gidana, sai ga wani mutum tsaye a gabana, yana saye da tufafi masu ɗaukar ido,