4 Shi kuwa ya zura masa ido a tsorace, ya ce, “Ya Ubangiji, mene ne?” Mala'ikan kuma ya ce masa, “Addu'arka da sadakarka sun kai har a gaban Allah, abubuwan tunawa ne kuma a gare shi.
5 To, yanzu, sai ka aiki mutane Yafa su kirawo Saminu, wanda ake kira Bitrus,
6 ya sauka a gun Saminu majemi, wanda gidansa yake a bakin bahar.”
7 Da mala'ikan da ya yi masa magana ya tafi, ya kira barorinsa biyu, da kuma wani soja mai ibada daga cikin waɗanda suke yi masa hidima kullum.
8 Da ya ba su labarin kome, ya aike su Yafa.
9 Kashegari suna cikin tafiya, sun zo kusa da gari ke nan, sai Bitrus ya hau kan soro yin addu'a, wajen rana tsaka.
10 Yunwa ta kama shi, har ya so ya ci wani abu. Ana cikin shirya abincin, sai wahayi ya zo masa,