1 A lokacin nan kuwa sarki Hirudus ya fara gwada wa waɗansu 'yan Ikkilisiya tasku,
2 har ma ya sare Yakubu ɗan'uwan Yahaya da takobi.
3 Da ya ga abin ya ƙayatar da Yahudawa, har wa yau kuma ya kama Bitrus, shi ma. Kwanakin idin abinci marar yisti ne kuwa.
4 Da ya kama shi, ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, su yi tsaronsa, da niyyar kawo shi a gaban jama'a bayan idin.
5 Sai aka tsare Bitrus a kurkuku, Ikkilisiya kuwa ta himmantu ga roƙon Allah saboda shi.
6 A daren da in gari ya waye Hirudus yake da niyyar fito da shi a yi masa hukunci, Bitrus kuwa na barci a tsakanin soja biyu, ɗaure da sarƙa biyu, masu tsaro kuma suna bakin ƙofa suna tsaron kurkukun,