2 Sa'ad da suke yi wa Ubangiji ibada, suna kuma yin azumi, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Sai ku keɓe mini Barnaba da Shawulu domin aikin da na kira su a kai.”
3 Bayan kuma sun yi azumi, sun kuma yi addu'a, sai suka ɗora musu hannu, suka sallame su.
4 Su kuwa, da Ruhu Mai Tsarki ya aike su, suka tafi Salukiya, daga can kuma suka shiga jirgin ruwa sai tsibirin Kubrus.
5 Da suka kai Salamis, suka sanar da Maganar Allah a majami'un Yahudawa, ga kuma Yahaya na taimakonsu.
6 Bayan sun zazzaga tsibirin duka har Bafusa, suka iske wani mai sihiri, annabin ƙarya, Bayahude, mai suna Bar-yashu'a,
7 Wanda yake tare da muƙaddas Sarjiyas Bulus, mutum mai basira. Sai muƙaddashin ya kira Barnaba da Shawulu ya nemi jin Maganar Allah.
8 Amma Alimas mai sihirin nan, (don wannan ita ce ma'anar sunansa), ya mūsa musu, yana neman bauɗar da muƙaddashin nan daga bangaskiya.