3 Sai Bulus da Barnaba suka daɗe a nan ƙwarai, suna wa'azi gabagaɗi bisa ga ikon Ubangiji, shi da ya shaida maganar alherinsa ta yarjin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi ta hannunsu.
4 Amma mutanen birni suka rarrabu, waɗansu suka koma bayan Yahudawa, waɗansu kuma bayan manzannin.
5 Sa'ad da al'ummai da Yahudawa tare da shugabanninsu suka tasar wa manzannin, su wulakanta su, su jejjefe su da duwatsu,
6 suka sami labari, suka gudu zuwa biranen Likoniya wato Listira da Darba, da kuma kewayensu.
7 Nan suka yi ta yin bisharar.
8 To, a Listira akwai wani mutum a zaune, wanda ƙafafunsa ba su da ƙarfi, gurgu ne tun da aka haife shi, bai ma taɓa tafiya ba.
9 Yana sauraron wa'azin Bulus, sai Bulus ya zuba masa ido, da ya ga bangaskiyarsa ta isa a warkar da shi,