1 Sai kuma Bulus ya zo Darba da Listira. Akwai wani almajiri a Listira, mai suna Timoti, ɗan wata Bayahudiya mai bi, ubansa kuwa Bahelene ne.
2 Shi kuwa 'yan'uwan da suke Listira da Ikoniya na yabonsa.
3 Sai Bulus ya so Timoti ya rako shi, har ya yi masa kaciya saboda Yahudawan da suke waɗannan wurare, don duk sun san ubansa Bahelene ne.
4 Lokacin da suke tafiya suna bin gari gari, suka riƙa gaya wa jama'a ƙa'idodin da manzanni da dattawan Ikkilisiya suka ƙulla a Urushalima, don su kiyaye su.
5 Ta haka ikilisiyoyi suka ƙarfafa a cikin bangaskiya, a kowace rana suna ƙara yawa.