17 Da muka zo Urushalima, 'yan'uwa suka karɓe mu da murna.
18 Kashegari Bulus ya tafi tare da mu wurin Yakubu, dattawan Ikkilisiya kuwa duk suna nan.
19 Bayan da ya gaisa da su, sai ya shiga bayyana musu filla filla abubuwan da Allah ya yi a cikin al'ummai ta wurin hidimarsa.
20 Su kuwa da suka ji haka, suka ɗaukaka Allah. Suka ce wa Bulus, “To, kā gani ɗan'uwa, dubban mutane sun ba da gaskiya a cikin Yahudawa, dukansu kuwa masu himma ne wajen bin Shari'a.
21 An kuwa sha gaya musu labarinka, cewa kai ne kake koya wa dukan Yahudawan da suke cikin al'ummai su yar da Shari'ar Musa. Wai kuma kana ce musu kada su yi wa 'ya'yansu kaciya, ko kuwa su bi al'adu.
22 To, ƙaƙa ke nan? Lalle za su ji labarin zuwanka.
23 Saboda haka sai ka yi abin da za mu faɗa maka. Muna da mutum huɗu da suka ɗauki wa'adi.