5 Amma da lokacin tashinmu ya yi, muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu, dukansu kuma har da matansu da 'ya'yansu, suka raka mu bayan gari, sa'an nan muka durƙusa a kan gaci, muka yi addu'a, muka yi bankwana da juna.
6 Sai muka shiga jirgi, su kuma suka koma gida.
7 Da muka gama tafiyarmu daga Taya, muka isa Talamayas, muka gaisa da 'yan'uwa, muka kuma kwana ɗaya a wurinsu.
8 Kashegari muka tashi muka zo Kaisariya, muka shiga gidan Filibus mai yin bishara, wanda yake ɗaya daga cikin bakwai ɗin nan, muka sauka a wurinsa.
9 Shi kuwa yana da 'ya'ya huɗu 'yan mata, masu yin annabci.
10 To, muna nan zaune 'yan kwanaki, sai wani annabi, mai suna Agabas, ya zo daga Yahudiya.
11 Da ya zo gare mu, ya ɗauki ɗamarar Bulus ya ɗaure kansa sawu da hannu, ya ce, “Ga abin da Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su ɗaure mai wannan ɗamara, su kuma bashe shi ga al'ummai.’ ”