1 Sai Bulus ya zuba wa majalisar ido ya ce, “Ya ku 'yan'uwa, bautar Allah nake yi da lamiri mai kyau har ya zuwa yau.”
2 Sai Hananiya babban firist ya umarci waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa.
3 Sai Bulus ya ce masa, “Kai munafiƙi, kai ma Allah zai buge ka! Ashe, wato kana zaune kana hukunta ni bisa ga Shari'a ne, ga shi kuwa kana yin umarni a doke ni, a saɓanin Shari'a?”
4 Sai waɗanda suke tsaye a wurin suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?”