16 To, ɗan 'yar'uwar Bulus ya ji labarin farkon da za su yi, ya kuma je ya shiga kagarar soja ya gaya wa Bulus.
17 Bulus kuwa ya kira wani jarumi ya ce, “Ka kai saurayin nan wurin shugaba, yana da wata magana da zai faɗa masa.”
18 Sai jarumin ya ɗauki saurayin ya kai shi gun shugaba, ya ce, “Ɗan sarƙan nan, Bulus, ya kira ni, ya roƙe ni in kawo saurayin nan a wurinka, don yana da wata maganar da zai gaya maka.”
19 Sai shugaban ya kama hannun saurayin, ya ja shi a waje ɗaya, ya tambaye shi a keɓance, “Wace magana za ka gaya mini?”
20 Yaron ya ce, “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kai musu Bulus majalisa gobe, kamar suna so su ƙara bincika maganarsa sosai.
21 Amma kada ka yardar musu, don fiye da mutum arba'in daga cikinsu suna fakonsa, sun kuma yi rantsuwa a kan ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe shi. Yanzu kuwa a shirye suke, yardarka kawai suka jira.”
22 Sai shugaban ya sallami saurayin ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa cewa ka sanar da ni maganar nan.”