5 Sai Bulus ya ce, “Ai, ban sani shi ne babban firist ba, 'yan'uwa, don a rubuce yake cewa, ‘Kada ka munana shugaban jama'a.’ ”
6 Amma da Bulus ya ga sashe ɗaya Sadukiyawa ne, ɗayan kuma Farisiyawa, ya ɗaga murya a majalisar ya ce, “Ya 'yan'uwa, ni ma Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ga shi kuwa, saboda na sa zuciya ga tashin matattu ne ake yi mini shari'a.”
7 Da ya faɗi haka sai gardama ta tashi a tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, har taron ya rabu biyu.
8 Sadukiyawa sun ce, wai ba tashin matattu, ba kuma mala'iku, ko ruhu. Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.
9 Sai ƙasaitacciyar hargowa ta tashi, waɗansu malamai kuma na ɗariƙar Farisiyawa suka miƙe a tsaye, suka yi ta yin matsananciyar jayayya, suna cewa, “Mu ba mu ga laifin mutumin nan ba. In wani ruhu ne ko mala'ika ya yi masa magana fa?”
10 Da gardamar ta yi tsanani, don gudun kada su yi kaca-kaca da Bulus, shugaban ya umarci sojan su sauka su ƙwato shi daga wurinsu ƙarfi da yaji, su kawo shi a kagarar soja.
11 Da daddare sai Ubangiji ya tsaya a kusa da Bulus, ya ce, “Ka yi ƙarfin hali, don kamar yadda ka shaide ni a Urushalima, haka kuma lalle ne ka shaide ni a Roma.”