3 kullum muna yarda da haka ƙwarai a ko'ina, tare da godiya ba iyaka.
4 Amma don kada in gajiyad da kai, ina roƙonka a cikin nasiharka, ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabinmu.
5 Mun tarar da mutumin nan fitinanne ne, yana ta da hargitsi tsakanin Yahudawa ko'ina a duniya, shi kuma ne turun ɗariƙar Nazarawa.
6 Har ma yana nema ya tozarta Haikali, amma muka kama shi. [Niyyarmu ce mu hukunta shi bisa ga shari'armu.
7 Amma shugaba Lisiyas ya zo ya ƙwace shi daga hannunmu ƙarfi da yaji,
8 ya yi umarni masu ƙararsa su zo a gabanka.] In kuwa ka tuhume shi da kanka, za ka iya tabbatarwa daga bakinsa duk ƙarar da muke tāsarwa.”
9 Yahudawa ma suka goyi bayan haka, suna tabbatarwa haka abin yake.