24 Sai Festas ya ce, “Ya sarki Agaribas, da dukan mutanen da suke tare da mu, kun ga mutumin nan da duk jama'ar Yahudawa suka kawo mini ƙararsa a Urushalima, da kuma nan, suna ihu, bai kamata a bar shi da rai ba.
25 Amma ni ban ga abin da ya yi wanda ya isa kisa ba. Tun da kuma shi kansa ya nema a mai da shari'arsa a gaban Augustas, ƙudura in aika da shi zuwa wurinsa.
26 Amma ba ni da wata tabbatacciyar magana da zan rubuta wa ubangijina game da shi. Saboda haka na kawo shi a gabanku, musamman kuwa a gabanka, ya sarki Agaribas, don bayan an yi bincike, ko na abin da zan rubuta.
27 Don ni, a ganina, wauta ce a aika da ɗan sarƙa, ba tare da an nuna laifofin da ya yi ba.”