1 Daga nan, sai Agaribas ya ce wa Bulus, “An ba ka izinin yin magana.”Sa'an nan fa Bulus ya ɗaga hannu, ya fara kawo hanzarinsa ya ce,
2 “Lalle na yi arziki, ya sarki Agaribas, da yake a gabanka ne zan kawo hanzarina yau a game da duk ƙarata da Yahudawa suka yi,
3 musamman da yake gwani ne kai ga sanin al'adun Yahudawa da maganganunsu. saboda haka, ina roƙonka ka saurare ni da haƙuri.
4 “Irin zaman da na yi tun daga ƙuruciyata, wato tun da farko, a cikin jama'armu da kuma a Urushalima har ya zuwa yau, sananne ne ga dukan Yahudawa.