26 Kashegari kuma waɗansu suna faɗa, sai ya nemi shirya su, ya ce, ‘Ku jama'a, ku 'yan'uwa ne fa, don me kuke cutar juna?’
27 Amma mai cutar ɗan'uwa nasa ya ture Musa, ya ce, ‘Wa ya sa ka shugaba da alƙali a kanmu?
28 Wato kana so ne ka kashe ni kamar yadda ka kashe Bamasaren nan na jiya?’
29 Da jin wannan magana, Musa ya gudu ya yi baƙunci a ƙasar Madayana, inda ya haifi 'ya'ya biyu maza.
30 “To, bayan shekara arba'in, wani mala'ika ya bayyana a gare shi cikin harshen wuta, a wani kurmi a jejin Dutsen Sina'i.
31 Da Musa ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya matso domin ya duba, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce,
32 ‘Ni ne Allahn kakanninka, Allahn Ibrahim da Ishaku da Yakubu.’ Sai jikin Musa ya ɗauki rawa, bai kuma iya ƙarfin halin dubawa ba.