2 da Aufiya 'yar'uwarmu, da Arkibus abokin famanmu, da kuma ikkilisiyar da take taruwa a gidanka.
3 Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.
4 A kullum ina gode wa Allahna duk sa'ad da nake yi maka addu'a,
5 saboda nakan ji labarin ƙauna da bangaskiya da kake yi wa Ubangiji Yesu da dukkan tsarkaka.
6 Ina addu'a bangaskiyar nan da ta haɗa ku, tă kasance mai ƙwazo a wajen ciyar da sanin dukkan kyawawan abubuwan da suke namu, saboda Almasihu.
7 Na yi farin ciki ƙwarai, zuciyata kuma ta ƙarfafa saboda ƙaunar da kake yi, yă kai 'dan'uwana, domin zukatan tsarkaka sun wartsake ta dalilinka.
8 Saboda haka, ko da yake saboda Almasihu ina iya umartarka gabagaɗi, ka yi abin da ya wajaba,