7 Na yi farin ciki ƙwarai, zuciyata kuma ta ƙarfafa saboda ƙaunar da kake yi, yă kai 'dan'uwana, domin zukatan tsarkaka sun wartsake ta dalilinka.
8 Saboda haka, ko da yake saboda Almasihu ina iya umartarka gabagaɗi, ka yi abin da ya wajaba,
9 duk da haka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu,
10 ina roƙonka saboda ɗana Unisimas, wanda na zama ubansa ina ɗaure.
11 Dā kam, ba shi da wani amfani a wurinka, amma a yanzu, hakika yana da amfani a gare mu, ni da kai.
12 Ga shi nan, na komo maka da shi kamar gudan zuciyata.
13 Dā kam sona in riƙe shi a wurina, yă riƙa yi mini hidima a madadinka, muddin ina ɗaure saboda bishara.