1 In akwai ƙarfafawa a cikin Almasihu, in dai da ƙarfin rinjaye na ƙauna, in har da tarayyarku ga Ruhu, da soyayyarku da kuma tausayinku,
2 to, albarkacinsu ku cikasa farin cikina da zamanku lafiya da juna, kuna ƙaunar juna, nufinku ɗaya, ra'ayinku ɗaya.
3 Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali'u, kowa yana mai da ɗan'uwansa ya fi shi.
4 Kowannenku kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula har da ta ɗan'uwansa ma.
5 Ku ɗauki halin Almasihu Yesu,
6 wanda, ko da yake a cikin surar Allah yake, bai mai da daidaitakar nan tasa da Allah abar da zai riƙe kankan ce ba,
7 sai ma ya mai da kansa baya matuƙa ta ɗaukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin ɗan adam.