1 Saboda haka ya 'yan'uwana, ƙaunatattuna, waɗanda nake bege, ku da kuke abin farin cikina da abin taƙamata kuma, ku dage ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna.
2 Na gargaɗi Afodiya, na kuma gargaɗi Sintiki, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne.
3 Ya kai abokin bautata na hakika, ina roƙonka, ka taimaki matan nan, don sun yi fama tare da ni a al'amarin bishara, haka ma Kilemas da sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suke a rubuce a cikin Littafin Rai.
4 A kullum ku yi farin ciki da Ubangiji, har wa yau ina dai ƙara gaya muku, ku yi farin ciki.
5 Bari kowa ya san jimirinku. Ubangiji ya yi kusan zuwa.