15 Amma sa'ad da shi wannan da ya keɓe ni tun kafin a haife ni, ya kuma kira ni bisa ga alherinsa, ya ji daɗin
16 bayyana Ɗansa a gare ni, domin in sanar da shi ga al'ummai, ban yi shawara da ɗan adam ba,
17 ban kuma je Urushalima wurin waɗanda suka riga ni zama manzanni ba, sai nan da nan na je ƙasar Larabawa, sa'an nan na komo Dimashƙu.
18 Bayan shekara uku kuma sai na tafi Urushalima ganin Kefas, na kuwa kwana goma sha biyar a gunsa.
19 Amma ban ga ko ɗaya a cikin sauran manzanni ba, sai dai Yakubu ɗan'uwan Ubangiji.
20 Abin nan da nake rubuto muku fa, ba ƙarya nake yi ba, a gaban Allah nake faɗa.
21 Daga baya kuma, na tafi ƙasar Suriya da ta Kilikiya.