3 Alheri da salama na Allah Uba su tabbata a gare ku, da na Ubangijinmu Yesu Almasihu,
4 wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu, domin yă cece mu daga mugun zamanin nan, bisa ga nufin Allahnmu, wato Ubanmu.
5 Ɗaukaka tā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin.
6 Na yi mamaki yadda nan da nan kuke ƙaurace wa wanda ya kira ku, bisa ga alherin Almasihu, har kuna koma wa wata baƙuwar bishara,
7 alhali kuwa ba wata bishara dabam, sai dai akwai waɗansu da suke ta da hankalinku, suna son jirkitar da bisharar Almasihu.
8 Amma ko mu, ko kuma wani mala'ika daga sama, in waninmu zai yi muku wata bishara dabam da wadda muka yi muku, to, ya zama la'ananne!
9 Kamar yadda muka faɗa a dā, haka yanzu ma nake sāke faɗa, cewa kowa ya yi muku wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, to, yă zama la'ananne!