2 Abu ɗaya kaɗai zan tambaye ku. Kun sami Ruhu saboda bin Shari'a ne, ko kuwa saboda gaskatawa ga maganar da kuka ji?
3 Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Da kuka fara da Ruhu, ashe, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa?
4 Ashe, a banza kuka sha wuya iri iri? In dai har a banzan ne!
5 Wato, shi da yake yi muku baiwar Ruhu, yake kuma yin mu'ujizai a cikinku, saboda kuna bin Shari'a ne yake yin haka, ko kuwa saboda gaskatawa da maganar da kuka ji?
6 Haka ma Ibrahim “ya gaskata Allah, bangaskiyan nan tasa kuma, aka lasafta ta adalci ce a gare shi.”
7 Wato kun ga ashe, masu bangaskiya su ne 'ya'yan Ibrahim.
8 A cikin Nassi kuwa an hango, cewa Allah zai kuɓutar da al'ummai ta wurin bangaskiya, wato, dā ma can an yi wa Ibrahim bishara cewa, “Ta wurinka za a yi wa dukkan al'ummai albarka.”