13 Ku kuma da kuke matattu saboda laifofinku, marasa kaciya ta jiki, Allah ya raya ku tare da Almasihu, ya yafe mana dukkan laifofinmu,
14 ya kuma yanke igiyar nan ta Shari'a da ta ɗaure mu da dokokinta, ya ɗauke ta, ya kafe ta da ƙusa a jikin gicciyensa.
15 Ya ƙwace makaman masarauta da na masu iko, ya kunyata su a fili, da ya yi nasara a kansu a kan gicciyen.
16 Saboda haka, kada ku damu in wani ya zarge ku a kan abin da kuke ci, ko abin da kuke sha, ko kuwa kan rashin kiyayewar wani idi, ko tsayawar wata, ko Asabar.
17 Waɗannan kam, isharori ne kawai na abin da zai auku, amma Almasihu shi ne ainihinsu.
18 Kada ku yarda kowane mutum ya ɓata ku, da cewa shi wani abu ne saboda, ya ga wahayi, ya kuma lazamta da yin tawali'un ƙarya, in ji shi kuma yana yi wa mala'iku sujada. Irin wannan mutum kumbura kansa yake yi ba dalili, sai ta son zuciya irin na halin mutuntaka,
19 bai kuwa manne wa kan ba, wanda ta gare shi ne dukkan jiki yake amfana, yake kuma a haɗe, ta wurin gaɓoɓi da jijiyoyi, yake kuma girma da girman da Allah yake sawa.