1 Bayan wannan Ubangiji ya zaɓi waɗansu mutum saba'in, ya aike su biyu biyu, su riga shi gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da shi kansa za shi.
2 Ya ce musu, “Girbin na da yawa, amma masu yinsa kaɗan ne. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi ya turo masu girbi, su yi masa girbi.
3 To, sai ku tafi. Ga shi na aike ku kamar 'yan tumaki a tsakiyar kyarketai.
4 Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko burgami, ko takalma. Kada ku yi doguwar gaisuwa da kowa a hanya.
5 Duk gidan da kuka sauka, ku fara da cewa, ‘Salama alaikun mutanen gidan nan!’
6 In akwai da ɗan salama a gidan, to, salamarku za ta tabbata a gare shi. In kuwa babu, za ta komo muku.
7 Ku zauna a gidan, kuna ci kuna shan duk irin abin da suka ba ku, domin ma'aikaci ya cancanci ladansa. Kada ku riƙa sāke masauki.