8 Duk garin da kuka shiga, in an yi na'am da ku, ku ci duk irin abin da aka kawo muku.
9 Ku warkar da marasa lafiya da suke cikinsa, ku kuma ce musu, ‘Mulkin Allah ya kusato ku.’
10 Amma duk garin da kuka shiga ba a yi na'am da ku ba, sai ku zaga kwararo kwararo, kuna cewa,
11 ‘Ko da ƙurar garinku da ta ɗafe a jikin ƙafafunmu ma, mun karkaɗe muku. Amma duk da haka ku sani Mulkin Allah ya kusato.’
12 Ina dai gaya muku, a ran nan, za a fi haƙurce wa Saduma a kan garin nan.”
13 “Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, sun zauna sāye da tsumma, suna hurwa da toka.
14 Amma a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku.