1 Sa'an nan kuwa da dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, da farko ya yi magana da almajiransa. Ya fara cewa, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, makirci.
2 Ba abin da yake rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba.
3 Don haka, kome kuka faɗa a asirce, za a ji shi a sarari. Abin kuma da kuka yi raɗa a loloki, za a yi shelarsa daga kan soraye
4 “Ya ku masoyana, ina dai gaya muku, kada ku ji tsoron masu kisan mutum, bayan sun kashe kuwa, ba abin da za su iya yi.
5 Amma zan gaya muku wanda za ku tsorata. Ku ji tsoron wannan da in ya kashe, yana da ikon jefawa a cikin Gidan Wuta. Hakika, ina gaya muku, shi za ku ji tsoro!
6 Ashe, ba gwara biyar ne kobo biyu ba? Ko ɗayarsu kuwa Allah bai manta da ita ba.