5 Sa'an nan ya ce musu, “Misali, wane ne a cikinku in yana da jaki ko takarkari ya faɗa a rijiya ran Asabar, ba zai fitar da shi nan da nan ba?”
6 Sai suka kasa ba da amsar waɗannan abubuwa.
7 To, ganin yadda waɗanda aka gayyato sun zaɓi mazaunan alfarma, sai ya ba su misali ya ce,
8 “In an gayyace ka zuwa biki, kada ka zauna a mazaunin alfarma, kada ya zamana an gayyato wani wanda ya fi ka daraja,
9 wanda ya gayyato ku duka biyu kuma yă zo ya ce maka, ‘Ba mutumin nan wuri.’ Sa'an nan a kunyace ka koma mazauni mafi ƙasƙanci.
10 Amma in an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi ƙasƙanci, don in mai gayyar ya zo, sai ya ce maka, ‘Aboki, hawo nan mana.’ Za ka sami girma ke nan a gaban dukan waɗanda kuke zaune tare.
11 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”